DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.37 |Issue 1 | April 2025|
Hassan Muhammad
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Jihar Sakkwato.
Tsakure
A adabin baka na Hausawa, waƙa tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo da hikima. Waƙar baka na da salo da fasaha iri-iri, ciki har da ɓoyayyen saƙo. Ɗaya daga cikin salo mafi ƙayatarwa a waƙoƙin Kassu Zurmi shi ne amfani da ɓoyayyin taurari, wato bayani da yabon mutum ko hali cikin salo na ɓoyewa. Ɓoyayyin taurari a adabi na nufin wasu mutane ko halaye da aka bayyana cikin waƙa ta hanyar nuni ko alama, ba tare da an ambaci sunayen waɗanda suka aikata su kai tsaye ba. Hakan yana buƙatar basira da fahimtar yadda makaɗin ke sarrafa kalmomi cikin tsarin labari amma a sigar waƙa don bayyana su waye ne ɓoyayyin taurari. Wannan nazari da za a gudanar an yi masa suna da ‘Wasu |oyayyin taurari a wasu Waƙoƙin Kassu Zurmi’. Nazarin zai yi tsinkaye ne a wasu waƙoƙin makaɗin tare da fito da wasu ɗiyan waƙoƙi da makaɗin ya yi amfani da su, wanda a cikin su za a bayyana yadda makaɗin ya ambaci ɓoyayyen tauraro. Nazarin zai taƙaita ne ga waƙoƙi biyu na makaɗin, kuma da su ne za a yi ƙoƙarin fito da ƙudurin wannan maƙala. Waƙoƙin su ne ‘Waƙar Nomau Namagarya’ da ‘Waƙar Na Gidan Duwa Maidabo Gajere Mazaizan Duniya’.