DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.10  |Issue 1 | April 2025|

 Hadiza Salihu Koko, Muhammad Abubakar Bazar

Department of Hausa  Shehu Shagari College of Education Sokoto

Tsakure 

Sata a al’adar Bahaushe abin ƙyama ce, kuma abin gudu da idan aka kama mutum ya yi ta, to barin gari ya kama shi, saboda kunya, kuma ko ya bar garin ya bar wa zuriarsa abin faɗi daga ‘ya’ya har jikoki. Wannan ya sa sata ba ta da hurumi ko gindin zama a dukkan sha’anonin Bahaushe, amma sai aka wayi gari ana tsintar waƙoƙi da ake yi wa masu yin sata, watau ɓarayi ke nan. Ta kai har ana yabon dabarunsu (bajintarsu) da yi musu kirari kamar yadda ake yi wa sauran mutane. Da haka aka samu mawaƙa irin su Gambo da Kassu Zurmi da wasu mawaƙa suna yi wa ɓarayi waƙa. Wannan muƙala, ta zaƙulo yadda mawaƙi Kassu Zurmi ya fito da yanaye yanayen sata da nauointa da dabarun yin ta a cikin wasu waƙoƙinsa da ya yi wa ɓarayi duk da yake shi ba makaɗin ɓarayi ba ne, makaɗin tauri da farauta ne, sai dai a ce sha’awa da kwaɗayi suka ja shi ga yin waƙar ɓarayi. Don yana cewa “ba za ni talauci ba, tun da arnan dare na biki, wanda duy yas samu da ni”. Muƙalar kuma ta taɓo kirari da faɗakarwar da Kassu ke yi wa masu kaya a kan ɓarayi da dangantakar ɓarayi da ‘yan tauri da kuma alaƙar Kassu da ɓarayin. Muƙala ta kammala da cewa Kassu ya yi wa ɓarayi farin sani da har yake iya fito da dabarun da suke yi wajen yin sata, da kuma kwaɗayin abin hannunsu da yake yi wanda ya kai shi ga zuwa ci-rani a waƙar ɓarayi. Hasali ma, ya fi samun alheri ga ɓarayi fiye da ga ‘yan tauri, don ko Gambo mai waƙar ɓarayi yana cewa “ A ba ka yau a ba ka gobe, ɓarawo ɗai a hakan ga.” Ra’in da aka ɗora wannan nazarin shi ne, ‘Ra’in Madubin ƙyallaro Aladu. Rai ne wanda yake nuni da yadda akan yi amfani da adabi ko alada ko harshe a matsayin madubi don ƙyallaro aladun alumma kamar yadda Ado, (2017: 84) ya bayyana. Hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike sun haɗa da, sauraren waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi a MP da wayar salula da kuma, bitar wasu litattafai da kundaye da muƙalun da aka buga.