DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.5  |Issue 1 | April 2025|

Asma’u Bello Balarabe

Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari, Sakkwato

Tsakure 

Zuga wata hanya ce da mawaƙa suke amfani da ita domin karsashi ko ƙwazo na abin da ake son ya aikata. Mawaƙa na amfani da wannan salo a cikin waƙa domin su wasa su kuma zuga wanda suke yi wa waƙa. Kasancewar Kassu makaɗin maza, dole ne ya yi amfani da salon zuga domin ya kwarzanta mutanensa. A wannan muƙala, an kawo maanar zuga da ire-iren waƙoƙin Kassu Zurmi waɗanda ake samun zuga a cikinsu. An kuma kawo misalan waƙoƙin Kassu Zurmi guda takwas tare da kawo inda aka sami zuga a cikinsu. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan muƙal shi ne ta hanyar sauraren waƙoƙi a MP da wayar salula da kuma littattafai da aka wallafa a kan Kassu Zurmi.