DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.31 |Issue 1 | April 2025|
Adamu Mainasara
Sashen Koyar da Harsunan Afrika (Hausa Unit), Jami’ar Al-qalam Katsina
Tsakure
Makaɗa da mawaƙa suna amfani da hanyoyi daban-daban domin ƙarfafa jarumai tare da saka musu karsashi a wajen aiwatar ayyukan da suka haɗa da, farauta da tauri da sata da sauransu. Manufar wannan takarda ita ce zaƙulo nau’o’in zuga kamar yadda suka wanzu a waƙoƙin makaɗa Abubakar Kassu Zurmi. Daga cikin ire-iren zuga da akan samu akwai; ta yabawa da ta buwaya da ta ingizau da ta kariyau da kuma ta halayya. Ra’in da aka ɗora wannan nazari shi ne, “Ra’in Waƙar Baka Bahaushiya”wanda Gusau (2015) ya samar. Daga cikin hanyoyin da aka bi don samun nasarar wannan bincike akwai; zaƙulo wasu waƙoƙin marigayi Abubakar Kassu don kalato manufofin takardar. Haka kuma, an bibiyi wasu ayyukan magabata masu alaƙa da nazarin don samun ƙarin haske. Babu shakka wannan bincike ya gano, makaɗa Kassu yana yawan amfani da zuga ne don ƙarfafa zukatan maza a wajen aiwatar da ayyukansu na jarunta musamman ‘yan farauta da kuma ‘yan tauri. Sannan kuma, yana yawaita amfani da zuga ta ingizau fiye da sauran nau’o’in zuga. Kazalika, yakan yi zuga ta kariyau don nuna raunin abokan adawar gwarazansa. Keɓaɓɓun Kalmomi: Zuga da jaruntaka da farauta da tauri da kariyau da tunkuɗau da yabo da ingizau da kuma buwaya.