DOI:  https://doi.org/10.65760/kassu.i1.1    |Issue 1 | April 2025|

Abubakar Sani Sayaya
Kofar Sauri Katsina

An yi wa wannan takardar take da “ Tauri A Farfajiyar Tunanin Abubakar Kassu Zurmi”. An Gina ta ne da nufin fito da irin fashin baƙin da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa aladar Tauri a cikin waƙoƙinsa. Takardar an ginata ne ta hanyar nazartar wasu muhimman aiyukan da aka wallafa da waɗanda ba a wallafa ba. Haka kuma an nazarci wasu turakun waƙoƙin da Kassun ya gabatar, musamman waɗanda suke magana a kan Tauri da magungunan Tauri. Ganin cewa Kassu Zurmi ya naƙalci aladar Tauri ya sa aka ɗora wannan aiki a kan Karin maganar Hausawa da ake cewa “Masu abi su ke da abinsu”. An yi tsokaci ne a kan irin fashin baƙin da Kassun ya yi wa aladar Tauri acikin sassa guda uku. A sashe na farko an yi tsokaci a kan maanar kalmomin da suka haɗa da Tauri da Farfajiya da kuma Tunani tare da bibiyar ire-iren magungunan da ‘yan tauri ke amfani da su, da wasu kalmomi da Kassu ya yi amfani da su a mamadin maganin tauri da kuma yadda ake amfani da magungunan. Sashe na biyu an yi tsokaci ne a kan irin hangen da Kassu ya yi wa al’adar tauri. A sashe na uku an gabatar da shawarwari da ake ganin sun dace. An gabatar da sawarwarin ne ta hanyar tuntuɓar wasu turakun waƙoƙin shi Kassu Zurmi ɗin. Sakamakon da aka samu yayin gina wannan takaarda ya tabbatar da cewa makaɗa Kassu Zurmi ya taskace al’adar tauri kafin rasuwarsa.