DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.3 |Issue 1 | April 2025|
Aminu A. Ibrahim, Abubakar Ɗanillela
Sashen Hausa na Kwalejin Ilimi, Shehu Shagari Sokoto
Tsakure
Hausawa kan ce “Yaba kyauta tukuici” kyauta wata ɗabi’a ce mai kyau wadda ake girmama mai yinta da sonsa cikin al’umma. Wannan maƙala ta dubi waƙoƙin makaɗa Kassu Zurmi domin tsakulo ire-iren kyautukan da yake bayyanawa a cikin waƙoƙin da yake yi wa gwarazansa. Wannan maƙalar ta bayyana hikimar Kassu Zurmi wajen bayyana kyautar da yake samu ga Gwarazansa domin ya bayyanasu ba marowata ba ne. Wannan maƙalar ta bi ra’in Gusau (1983) in da ya yi amfani da shi kan nazarin waƙar baka Bahaushiya musamman wadda ta yi bayani dangane da adabin baka da maganganun hikima. Haka kuma wannan maƙalar ta bi hanyar sauraren waƙoƙin Kassu cikin kaset- kaset da kuma waɗanda ta samo daga da littafin da magaji (2016) ya rubuta da kundin digiri na biyu na Habib Ƙaura (2017) wajen samun waɗanna waƙoƙin.