DOI: https://doi.org/10.65760/kassu.i1.17 |Issue 1 | April 2025|
Ibrahim Muhammad
Danmadamin Birnin Magaji Inkiya Fadar Mai Martaba Ɗan’alin Birnin Magaji, Birnin Magaji Jihar Zamfara, Jihar Zamfara Nijeriya
Tsakure
Kassu fitacce ne a waƙoƙin, noma, farauta, tauri da ɗan’hali. Shi ya sa aka kira shi makaɗin Maza. Ba a kalli Maza a matsayin jinsi ba a nan, sai dai masu ƙarhin hali wajen murza wasu ayyuka masu wuya ta fuskar gwarzontaka. Wanda ko ya koma daji ya tare a muhalli ɗaya da miyagun ƙwari da namun daji waɗanda Allah ya keɓe su a dajin, da wanda ya wulaƙanta darensa da ranarsa domin ya firgita wanda ya samu halaliyarsa a tsakiyar daren da rana ya kwace masa ƙotonsa, wato mai ɗan hali, in aka haɗa da wanda kullum tunaninsa bai fi nuna buwaya ba a bayyane da ɓoye ba, wato Dantauri, to waɗannan su ne Kassu ya shahara wajen yi ma waƙa. Na daɗe ina tattara waƙoƙin Kassu. Na mayyeze ƙumshiyarsu kamar yadda nissan Kassun shi kansa. Na sha binsa ina neman tafsirin fasaharsa tun ina Dankachaurana. Na ga lokaci ya yi da zan ɓarge gumina domin tabbatar ma ɗalibai ‘yan uwana cewa Kassu fasihi ne ta fuskar adana tarihin waɗanda suka yi sunan su maza ne musamman a cikin al’ummarsa. Wannan tsakure zai taƙaita kansa ne a nazarin wata karabkiyar da ta wanzu tsawon zamunna tsakanin ‘yan Tauri na yankin da shi mawaƙin ya yi nasa zamani. Sai mun haɗu a cikin zubin wannan maƙala domin ku sha labari.
Keɓaɓɓun Kalmomi: Wawa Mugunyar Tsirfa, Uba na Fada Uwa na Kuka: Lalaben Tarihin Karabkiya Tsakanin ‘Yan Tauri a Bakin Makaɗa Kassu Zurmi. Bitar Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa